Harajin Trump: Kasashen Afirka na shirin tunkarar tasirin matakin
AFIRKA
5 minti karatu
Harajin Trump: Kasashen Afirka na shirin tunkarar tasirin matakinTun bayan sanarwar karin haraji da Trump ya yi, kasashen Afirka ma, na fuskantar rikitaccen yanayi da kalubale, inda kowacce kasa ke neman mafita ta hanyar aiwatar da wasu dabaru da za su hana ta illatuwa daga tasirin matakin.
Kasashen Afirka na fuskantar yanayin mai cike da kalubale da ke da rikitarwa / Others
10 Afrilu 2025

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya ce ba zai janye daga matakin da ya dauka na lafta karin haraji kan kayan da ake shiga da su kasar daga kasashen waje ba, duk da girgiza kasuwanni da matakin nasa ya yi, ana fargabar samun durkushewar hada-hada a kasuwancin duniya.

A yayin da Trump ke ikirarin cewa shugabannin duniya na “fafutuka don ƙulla yarjejeniya” da Amurka, matakin nasa ya bar kasashe da dama na faman yadda za su mayar da martani.

Kasashen Afirka ma na fuskantar rikitaccen yanayi da kalubale, inda kowacce kasa ke neman mafita ta hanyar aiwatar da wasu dabaru da za su hana ta illatuwa daga tasirin matakin.

An tunkari tsarin lafta karin harajin na Trump da daakar matakai irin na yadda ya sanar da ƙara harajin, “Babu wata tattaunawa har sai sun biya mu kudade a kowacce shekara,” wanda ke bayyana samun sauyi daga tattaunawar diflomasiyya da aka saba gani.

Amurka ta ce sama da kasashen duniya 50 sun tuntubi gwamnatin Trump da ta sulhunta kan karin harajin, wanda ke bayyana tsananin damuwa a kowanne yanki da kuma babban sauyin da za a samu a fagen kasuwancin duniya.

Matakan da Zimbabwe ta dauka

Shugaban Kasar Zimbabwe Emmerson Mnanggwa ya dauki babban mataki, ya sanar da janye duk wani haraji daga kayan da ake shigarwa kasar daga Amurka domin habaka kai kayan Amurka kasar da kai na kasarsa zuwa Amurka. A karkashin sabon tsarin Trump, Zimbabwe na fuskantar karin kashi 18 na haraji.

“Wannan mataki na da manufar fadada shigar da kayan Amurka kasuwannin Zimbabwe da kuma ƙara yawan kayan da Zimbabwe ke kai wa Amurka. Wannan mataki na bayyana aniyarmu ta samar da yanayi na adalci a kasuwanci da habaka hadin-kai.

Tawagar Lesotho ta garzaya zuwa Amurka

A wajen Lesotho, lamarin mummunan mataki ne. A yayin da kashi 45 na kayan da take fitarwa mafi yawan na tufafi ke tafiya zuwa Amurka ne, a yanzu kasar na shirin fuskantar kashi 50 na haraji daga Amurka.

Wannan na iya nakasta kusan kashi 50 na kayayyakin da Lesotho ke fitarwa kasashen waje.

Ministan Kasuwanci Mokhethi Shelile ya tattara tawaga da za ta tattauna kai tsaye da Amurka da rage radadin da wannan mataki zai kawo ga kasarsu.

Alkaluman na da muni sosai: Kayan da Lesotho ke kai wa Amurka ya kai na dala miliyan 237 a 2024, wanda ya kai yawan ninki goma na kudaden da suke samu a cikin gida.

Sabon harajin na barazana sosai ga tattalin arzikin kasar.

Matakin taka tsan-tsan na Afirka ta Kudu

Afirka ta Kudu, babbar mai taka rawa a nahiyar Afirka, na daukar matakin kariya. Maimakon mayar da martani nan da nan, kasar ta mayar da hankali da bayar da fifiko ga togaciya da kulla yarjejeniya me za a kai a kawo.

“Sun lafta haraji, mu kuma muna nazari kan tasirin harajin a kanmu, …. kuma za mu yi kokarin bayyana matsayinmu,” Ramaphosa ya fada wa ‘yan jaridar kasar a wajen taron jam’iyyar ANC a ranar Lahadi.

Karin kashi 31 na haraji kan kayan Afirka ta Kudu da ake kai wa Amurka ya kawo damuwa game da rasa alfanu a karkashin Dokar Damarmakin Habakar Afirka (AGOA) - wani tsari da ya togaje wasu kasashen Afirka daga biyan haraji kan wasu kayayyaki da suke kai wa Amurka.

Madagascar, daya daga kasashen duniya mafiya talauci a duniya,, na fuskantar haraji da kashi 47 kan kayan da take shigarwa Amurka na dala miliyan 733.

Gwamnatin na tattaunawa da Amurka ta hanyoyin diflomasiyya da kasuwanci, tana neman a sake duba yawan harajin.

A yayin da hakan ke faruwa, ana tirsasa kasashen Afirka su fadada yanayin fitar da kayayyakinsu zuwa kasashen waje ta hanyar neman damarmaki.

Kiran a farka daga Nijeriya

Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari na Nijeriya, Jumoke Oduwole, ya yi tsokaci game da lafta harajin inda ya ce kasar “ta dauki Amurka a matsayin abokiyar kasuwanci da zuba jari mai daraja, da suke da manufofi iri guda na cigaban tattalin arziki.”

Sanarwar ta Oduwale ta kuma yi kira ga kasashen Afirka da su ƙarfafa kasuwanci a tsakanin kasashen nahiyar.

“Tana kuma kira ga kasashen Afirka - da Nijeriya da su karfafa kasuwanci a tsakaninsu ta hanyar amfani da yarjejeniyar AfCTA, suna karfafa yadda Nijeriya ke hanzarta aiwatar da yarjejeniyar, su zurfafa hadewar yankunansu, da samar da tsare-tsare kamar na Tsarin Biyan Kudade a Dukkan Afirka (PAPSS) don saukaka tsadar gudanar da kasuwanci da habaka kasuwanci a cikin nahiyar,“ in ji Oduwale.

Kira ga fadada kasuwanci da mu’amala

Lafta harajin da Amurka ta yi ya zama tunatarwa game da raunin da ke tattare da dogaro kan wajen fitar da kaya kwaya daya kawai.

A yanzu dole ta sanya kasashen Afirka su fadada hanyoyin fitar da kayayyakinsu da kulla sabbin huldodin kasuwanci da karin damarmaki.

Masu nazari na cewa wannan sauyi ba wai matakin kawo gyara ba ne, zai zama matakin riga-kafi don samar da tattalin arziki mafi karfi.

Sakamakon wadannan kokari zai haifar da tasiri babba ga makomar tattalin arzikin wadannan kasashe.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us