Yadda kawancen tsaron Turkiyya da Nijeriya ke taimaka wa wajen yaƙi da ta’addanci
AFIRKA
5 minti karatu
Yadda kawancen tsaron Turkiyya da Nijeriya ke taimaka wa wajen yaƙi da ta’addanciFasahar Turkiyya wajen kera kayan tsaro da hadin kai na taimaka wa Nijeriya yaki da ta’addanci, inda ake samun sabon kawancen tsaro a Afirka.
Nijeriya na kashe makudan kudade wajen ayyukan soji a duk shekara. / AA
5 Agusta 2025

Daga Charles Mgbolu da Abdulbaki Jari

Manufar babban titin Abuja zuwa Kaduna, wanda yake hada babban birnin Najeriya da daya daga cikin manyan biranen arewacin kasar, ita ce ya zama wata alamar taswirar samar da ababen more rayuwa da cigaba a kasar mafi yawan al'uma a Afirka.

A maimakon haka, wannan hanya mai tsawon kilomita 160 ta zama jigon yakin da Najeriya ke yi da matsalar garkuwa da mutane domin neman kudin fansa a kan manyan tituna.

Jiragen saman BAHA da Turkiyya ke kera a yanzu suna sintiri a sararin samaniya, yayin da manyan motocin YÖRÜK 4X4 ke bayar da tsaro a kan hanyar. Wannan dai wani bangare ne na karfafa hadin gwiwar tsaro da Turkiyya da Najeriya, wanda ke kunshe a cikin wani shiri na miliyoyin daloli na shigar da kwareewar Turkiyya da kayayyakinta ga dabarun samar da tsaro.

Ta wata mahangar kuma, hakan na nuna gagarumin sauyi a yadda Nijeriya – da yawancin yammacin Afirka – ke tunkarar rikicin tsaro a cikin gida.

Kayayyakin tsaron da Turkiyya ke fitarwa zuwa Afirka ya karu daga dalar Amurka miliyan 82.9 a shekarar 2020 zuwa dala miliyan 460.6 a shekarar 2021, wanda hakan ke nuna karuwar sha'awar na'urorin sojan Turkiyya har ninki biyar, a cewar wani bincike da kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya yi.

Yanayin ya wuce batun farashi mai kyau. Ba kamar masu samar da kayayyaki na yammacin Turai da ke sanya sharadi kan sayar da makamai da kuma amfani da su ba, Turkiyya na bayar da abin da masu sharhi suka kira manufa "ba tare da sharadi ba", wanda hakan ke bai wa kasashen Afirka damar ci gaba da cin gashin kansu kan sha’anin tsaro.

Mallakar jiragen sama masu saukar ungulu samfurin T-129 ATAK guda shida da Najeriya ta yi a 2024 daga kamfanin TAI na Turkiyya, na bayyana wani bangare na babban lamarin. Turkiyya ta rattaba hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa na soji da kasashen Afirka sama da 20, gami da bude ofisoshin jakadanci 44 a fadin nahiyar - daga 12 kacal a shekarar 2002.

Karamin Ministan Tsaron Najeriya Bello Muhammad Matawalle ya shaidawa TRT Afrika cewa, “Ministan tsaron kasar Turkiyya ya yi alkawarin ba mu gurabe domin wasu jami’an sojin mu su kai ziyara kasar domin samun horo, musamman a fannin jiragen sama, da na’urorin leken asiri, da kuma kara karfin sojojin Najeriya.

Matawalle, wanda ya halarci bikin baje-kolin masana'antun tsaro na kasa da kasa karo na 17 na shekarar 2025 daga ranar 22 zuwa 27 ga watan Yuli a birnin Istanbul, ya yi imanin cewa, hadin gwiwar tsaro da Turkiyya ya kawo sauyi a yakin da Najeriya ke yi da ta'addanci, 'yan fashi da sauran nau'ikan tashe-tashen hankula.

Kasa mai aman jini

A arewacin kasar, 'yan ta'addar Boko Haram da Daesh sun shafe shekaru 15 suna tashe-tashen hankula, yayin da 'yan bindiga suka mayar da garkuwa da mutane zuwa masana'antu.

Sauyin yanayi ya tsananta rigingimun manoma da makiyaya wanda a yanzu ya yadu daga jihohin arewa masu nisa zuwa kudancin Nijeriya, yayin da matsalar tabarbarewar albarkatu ke kara kamari.

A yankin kudu maso gabas, kungiyar masu fafutukar neman kafa kasar Biafra (IPOB) da reshenta masu dauke da makamai, wato Eastern Security Network (ESN) da gwamnati ta ayyana a matsayin 'yan ta'adda, na ta yaki, suna gurgunta harkokin tattalin arziki ta hanyar tashin hankali da kuma barazana.

Najeriya dai na kara kashe kudade a ayyukan soji duk shekara, amma har yanzu kwalliya ba biya kudin sabulu ba, sai dai a yanzu Turkiyya na son taimaka wa a kawo sauyi.

Fasahar kere-kere ta Turkiyya

Kamfanin kayan tsaro na Havelsan da ke Ankara ya sayar wa da Nijeriya jirage marasa matuka na BAHA wadanda ke iya tashi da sauka a kaikaice kuma suke habaka wa da inganta ayyyukan tsaro.

STM, daya daga cikin 'yan kwangilar kayan tsaro na sojojin Turkiyya, na fitar da kananan jirage marasa matuki da ake kira Togan zuwa kasashen waje.

Motoci masu sulke 4x4 sun fito ne daga Nurol Makina, yayin da Asisguard ke samar da sassan jiragen yaki marasa matuki na Songar da ke aiki da motocin.

Kimanin karin wasu 'yan kwangila goma na Turkiyya sun kara karfafa dangantakar samun kayan tsaron, wanda Matawalle ya bayyana a matsayin "hadin gwiwa mai albarka".

Haɗin gwiwar Turkiyya da Nijeriya ba a boye yake ba. A duk faɗin yankin Sahel, tasirin Turkiyya na ƙaruwa cikin sauri, yana bayar da mafita ga hanyoyin haɗin gwiwa da ƙasashen yamma waɗanda galibi ke bayar da farashi mai tsada ga ƙasashen Afirka.

Kamfanin dillancin labaran Anadolu ya rawaito jakadan Turkiyya a Nijar Mustafa Turker Ari na cewa kasarsa na bayar da tallafin kudi ga rundunar yaki da ta'addanci ta G5 Sahel - tsarin hadin gwiwa da ya kunshi kasashen Burkina Faso, Chadi, Mali, Mauritania da Nijar.

Kara shigar da Turkiyya ke yi na nuni da aniyar tabbatar da zaman lafiya a yankin fiye da yarjejeniya tsakanin kasashen biyu.

A kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, shugar da kayan aikin tsaro na Turkiyya a cikin matakan tsaro na Najeriya abu ne da ake wa kallon ya harua batun musayar fasahar kere-kere. Haka kuma, ya nuna an samu sauyi kan yadda kasashen Afirka ke hulda da kasashen waje, wadanda kawai suna neman abokan kawancen da za su ba da hadin kai ba tare da sunkuyar da kai ba.

Najeriya ta yi imanin cewa, kawancen tsaro da Turkiyya na samar da daidaito daban-daban na dadaddiyar matsalar da ke ci mata tuwo a kwarya.

Sai dai Matawalle ya jaddada cewa fasahar kere-kere kadai ba za ta magance matsalar tsaro a Najeriya ba, inda ya yi kira da a kara hada kai a cikin gida, musamman tattara bayanan sirri daga al'umomin yankunan da lamarin ya shafa, inda masu aikata laifuka da 'yan ta'adda sukan shiga cikin fararen hula domin gujewa jami'an tsaron da z asu gano su.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us