Yadda aka kama fiye da mutum 300 da ake zargi da zamba ta intanet a ƙasashen Afirka
AFIRKA
3 minti karatu
Yadda aka kama fiye da mutum 300 da ake zargi da zamba ta intanet a ƙasashen AfirkaHukumar ‘Yan Sanda Ta Ƙasa da Ƙasa, Interpol ce ta sanar da hakan a cikin sabon rahoton da ta fitar ranar Litinin, inda ta ce an yi kamen ne a wani ɓangare na samamen Operation Red Card da ta yi daga watan Nuwamban 2024 zuwa Fabrairun 2025.
Interpol ta ce laifukan da ta gano a lokacin samamen sun haɗa da fiye da mutum 5,000. / Others
25 Maris 2025

Hukukomi a ƙasashen Afirka bakwai sun kama mutum 306 da ake zargi da hare-haren intanet tare da ƙwace na’urori 1,842, a wani samame na ƙasa da ƙasa da aka yi da nufin daƙile duk wasu munanan ayyuka da suka shafi intanet kamar zamba da almundahana.

Hukumar ‘Yan Sanda Ta Ƙasa da Ƙasa, Interpol ce ta sanar da hakan a cikin sabon rahoton da ta fitar ranar Litinin, inda ta ce an yi kamen ne a wani ɓangare na samamen Operation Red Card da ta yi daga watan Nuwamban 2024 zuwa Fabrairun 2025.

Maƙasudin yin samamen shi ne don a rusa da lalata hanyoyin da masu aikata miyagun laifuka suke amfani da su a tsakaninsu daga ƙasashe daban-daban, lamarin da ke jawo mummunar cutarwa ga mutane da harkokin kasuwanci.

Su waɗannan miyagun ayyuka sun fi mayar da hankali ne a kan haƙon ayyukan manhajojin banki na intanet da zuba jari da manhajojin aika saƙon kar-ta-kwana na yaudara.

Interpol ta ce laifukan da ta gano a lokacin samamen sun haɗa da fiye da mutum 5,000.

Mafi yawan mutanen da aka kama ‘yan Nijeriya ne

A wani mataki na ɗabbaka wannan aiki, rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta kama mutum 130 da suka hada da ‘yan kasashen waje 113, bisa zarginsu da hannu a laifukan da suka shafi intanet, kamar caca da kuma damfara da sunan zuba jari, a cewar Interpol.

Wadanda ake zargin, wadanda suka mayar da kudaden da suka samu zuwa kadarori na dijital don ɓoye yadda za a gano su, sun fito ne daga kasashe daban-daban inda suke gudanar da haramtattun tsare-tsare a cikin yaruka da dama.

Hukumomin Nijeriya sun tabbatar da cewa wasu daga cikin mutanen da ke aiki a cibiyoyin damfara na iya zama wadanda aka yi safarar su ne, da tilasta musu aikata laifuka.

Gaba ɗaya binciken ya kai ga ƙwace motoci 26 da gidaje 16 da filaye 39 da kuma na’urori 685.

Afirka ta Kudu

A can Afirka ta Kudu ma, hukumomi sun kama mutum 40 tare da katunan waya na SIMfiye da 1,000, da komfuta 53 da sauran wasu na’urori.

Wannan shirin, wanda ke mayar da kiran waya na ƙasashen waje a matsayin na gida, yawancin masu laifi ke amfani da su don ƙaddamar da aika saƙonni na SMS na zamba masu yawa.

Gabanin aikin, kasashe sun yi musayar bayanan sirri kan muhimman wuraren da za a kai samamen.

Hukumar INTERPOL ce ta inganta wannan sirrin tare da fahimtar tsarin aikata laifuka ta hanyar amfani da bayanai daga abokan hulɗa na kamfanoni masu zaman kansu kamar su -Group-IB, Kaspersky da Trend Micro.

Aikin samamen ya haɗa ƙasashe bakwai ne na Afirka da suka hada da Benin da Cote d'Ivoire da Nijeriya da Rwanda da Afirka ta Kudu da Togo da kuma Zambia.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us