Me ya sa Turkiyya ke ƙarfafa dokokin zuwa yin jinya a ƙasar?
TURKIYYA
6 minti karatu
Me ya sa Turkiyya ke ƙarfafa dokokin zuwa yin jinya a ƙasar?Turkiyya na ƙarfafa dokoki domin ta saka ido kan ɓangaren zuwa jinya a ƙasar da ke bunƙasa, tare da burin samun dala biliyan $12 a matsayin kuɗin shiga a wannan shekarar.
Me ya sa Turkiyya ke ƙarfafa dokokin zuwa jinya a ƙasar? / AA
5 Afrilu 2025

Daga Esra Karataş AlpayEsra Karataş Alpay

Turkiyya na ƙaddamar da tsauraran dokoki da ƙa'idoji domin ziyarar majinyata zuwa cibiyoyinta domin neman lafiya, da suka haɗa da dashen gashi da aikin gyaran jiki, yayin da Ankara ke hanƙoron jaddada matsayinta a ɓangaren yawon shakatawa don neman lafiya mai tattare da biliyoyin kuɗaɗe.

Ma'aikatar kiwon lafiya ta Turkiyya ta gabatar da sabbin manufofi da ke buƙatar majinyata daga ƙasashen ƙetare su nemi inshorar kiwon lafiya ta tafiya domin yin kandagarkin abin da zai je ya komo sakamakon matakai na jinya.

Manufar, har wa yau, tana da hadafin tabbatarwa cibiyoyin kiwon lafiya na cika ƙaidojin aiki yayin da gwamnati ke da burin samun biliyan $12 a matsayin kuɗin shiga daga masu zuwa jinya a 2025, inda ake hasashen shigowar majinyata daga ƙetare miliyan 2.

"Turkiyya ta kafa kanta a matsayin jagora a duniya a fagen kai mata ziyara domin jinya," Farfesa Dr Ethem Guneren, wani gogaggen mai yin tiyatar gyaran jiki kuma mai yin hidima wa majinyata daga ƙetare, da gwamnati ta san da zamansa, ya sheda wa TRT World.

"Cibiyoyin kiwon lafiyarmu suna daga cikin mafi inganci a duniya, da suka ƙunshi ƙoƙoluwar fasaha haɗi da ƙwararrun ma'aikatan kiwon lafiya,"

A matsayin ɗaya daga cikin na gaba gaba a duniya a fagen yawon shakatawa domin neman lafiya, Turkiyya ta karɓi baƙi masu neman lafiya fiye da miliyan 1.5 a shekarar da ta gabata, ta samu aƙalla dala biliyan $3 a matsayin kuɗin shiga.

Ana sa rai girman fannin yawon shakatawa domin neman lafiya a duniya zai kai dala biliyan $127 zuwa shekarar 2028, kuma Turkiyya na da hadafin waftar kaso mai tsoka daga ciki.

Ba batun kuɗin ba ne kaɗai

Nasarar da Turkiyya ta samu a fagen yawon shakatawa don neman lafiya ya ginu ne bisa wasu muhimman ginshiƙai. rashin tsada, cibiyoyin kiwon lafiya masu inganci ƙwarai, ƙoƙoluwar fasahar zamani da kuma ma'aikatan kiwon lafiya da aka bai wa horo mafi inganci, ƙwararru suka faɗa.

Ƙasar tana daga cikin ƙasashen duniya guda biyar na gaba gaba a harkar ziyarar ta domin neman lafiya, inda take da cibiyoyin kiwon lafiya da duniya ta yarda da ingancinsu guda 40.

Majinyata daga Jamus,da Amurka, da Birtaniya, da Rasha,da Iraqi da Azerbaijan da kuma Gabas ta Tsakiya da ma wasu wuraren suna hallara a Turkiyya da yawansu, domin jinya kama daga aikin gyaran jiki da jinyar ciwon haƙora, da ta ido, da ta kansa, da dashen  gaɓɓai, da Kuma tiyatar rage ƙiba.

Ba baƙon abu ba ne ka ga baƙi na kai-komo a zauren otel kansu da hancinsu nannaɗe da bandeji da ke nuni da an yi musu tiyata.

Guneran, wanda ya samu horo daga ƙasar waje kuma ya samu gogewa sosai a aikin tiyatar sake fasalin halitta ko ƙara kyaun halitta, ya jaddada cewa nasarar Turkiyya ba ta taƙaita ga sauƙin kuɗin ba ne, har ma da ingancin aikin.

"Mene ne ya sa majinyata ke zaɓar zuwa Turkiyya? Ba wai don kawai jinyar ba ta fi ƙarfin aljihunsu ba ne. Gauraye ne na ingantaccen tsarin kiwon lafiya da kuma fasahar zamani mafi inganci da suka sanya ake rubibin mu," ya faɗa.

"Idan muka mayar da hankali kan farashi kaɗai, muna kasadar kassara kyakkyawan aikin da ke kawo majinyata nan tun da farko."

Turkiyya musamman ta shahara kan ƙwarewa wajen dashen gashi, ana saka ta a jerin jagororin duniya a wannan fagen.

Har wa yau, tana daga cikin wurare 10 da majinyata da ke buƙatar dashen gaɓɓai ke ziyarta.

Yanzu gwamnati na faɗaɗa tunaninta zuwa kan wasu fagen da ke tasowa kamar kula da tsufa, da ƙwayoyin halitta na musamman, da yin tiyata tare da taimakon mutum mutumi da kuma yawon shakatawa a yanayin zafi, sake jaddada hangenta na zama cibiyar kiwon lafiya ta duniya.

Dokoki masu ƙarfi domin bai wa majinyaci kariya

Sabuwar dokar za ta sa a samu ƙarin kulawa da gudanar da aiki yadda ya kamata tsakanin ma'aikatan kiwon lafiya da jami'an jinya da ke kula da majinyata daga wasu ƙasashen.

A ƙarƙashin waɗannan ƙa'idojin, cibiyar kiwon lafiya da masu aikin za su ɗauki cikakken alhaki game da ingancin aikin da ake samarwa.

Duk cibiyoyin kiwon lafiya da hukumomi su nemi izini a hukumance daga wajen Hukumar Kiwon Lafiya ta Ƙasa da Ƙasa (USHAS),  hukuma da ke da sahalewar gwamnati, da kuma maƙala katin sheda na "Hukumar Kiwon Lafiya ta Turkiyya" “HealthTürkiye” a harabobinsu.

Domin kyautata hidimar majinyaci, wajibi ne hukumomi da ke tsakani su samar da cibiyoyin kiran waya 24/7 da za a dinga kira a aƙalla harsuna biyu, domin tabbatar da sadarwa babu tangarɗa ga majinyatan ƙasashen waje.

USHAS za ta tabbatar an bi ƙa'idojin ta hanyar sa ido akai akai, kuma duk cibiyar da aka samu ta karya ƙa'idar za a ba ta kwanakin aiki 30 ta gyara. Idan ba ta yi gyaran ba za a iya janye lasisinta na yi wa ƴan ƙasar waje magani na tsawon watanni shida.

”Guneren ya yaba wa shirin, yana cewa, wajabta yin inshorar samun matsala muhimmin lamari ne. Ba zai taƙaita ga kyautata kula da lafiyar majinyaci ba kaɗai, zai kuma jaddada aminci a tsarin kiwon lafiyarmu."

Dokar har ila yau,ta yi umurnin cewa duk cibiyoyin kiwon lafiyar da ke hulɗa da majinyata daga ƙasashen waje, su samar da adireshin yanar gizo a harsuna fiye da ɗaya sannan su yi rigistar ayyukansu da shafin ma'aikatar a hukumance.

 Duba ga babban hoton

Turkiyya na kallon yawon shakatawa don neman lafiya a matsayin jigo ga tsarin bunƙasar tattalin arziƙinta, masana suka ce.

Hasashen gwamnati ya nuna cewa zuwa shekarar 2025, fagen zai samar da kuɗin shiga dala biliyan $10 - $12, sannan zuwa shekarar 2028, kuɗin shigar zai iya kai wa dala biliyan $20.

Amma banda nasara ta fannin kuɗi, hadafin shi ne a jaddada matsayin Turkiyya na kasancewa jagorar duniya wajen samar da kiwon lafiya.

"Yanzu Turkiyya ba jagorar yanki ba ce, face jagorar duniya ce wajen samar da kiwon lafiya," Guneren ya faɗa.

"Muna haɗa yin jinyar gargajiya ta Turkiyya tare da kiwon lafiyar zamani don bayar da fata nagari - ba ga mutanenmu ba kaɗai, har ga duniya gabaɗaya."

Idan aka ci gaba da zuba jari a asibitocin zamani, da bincike mai zurfi da kuma ƙwararrun ma'aikatan kiwon lafiya, Turkiyya a shirye take ta ci gaba da jaddada matsayinta a fagen yawon shakatawa domin neman lafiya.

"Duniya na amfana da ƙwarewar Turkiyya a fannin kiwon lafiya, kuma a shirye muke mu tabbatar da mataki mafi ƙoli wajen kulawa da mara lafiya," Guneren ya ce.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us