Yadda rayuwa ta kasance wa 'yan-sama-jannatin da suka maƙale a sararin samaniya tsawon wata tara
KIMIYYA DA FASAHA
6 minti karatu
Yadda rayuwa ta kasance wa 'yan-sama-jannatin da suka maƙale a sararin samaniya tsawon wata taraBayan shafe fiye da kwana 288 a sararin samaniya, ‘yan-sama-jannati Hukumar Binciken Sararrin Samaniya ta Amurka, NASA Butch Wilmore da Suni Williams sun komo duniyar Earth, inda suka jigata tuɓus kuma gangar jikinsu ta yi nauyi sosai.
'Yan-sama-jannati / Reuters
21 Maris 2025

Washington, DC — Zaman kusan shekara guda a sararin samaniya yana sauya jikin mutum ta hanyoyin da ba yawan shirin da zai sa su tunkari hakan. Jiki gaba ɗaya yana mantawa da nauyin maganaɗisun ƙasa. Tsokar jiki na sakewa. Ƙashi yana zama mara ƙarfi. Ƙarfin ganin idanu na raguwa.

Komawa duniya ba sauka a cikin Earth kawai yake nufi ba — abin ya haɗa har da gwagwarmayar dawo da jikin mutum yadda yake.

Tun da fari an tsara cewa ‘yan-sama-jannatin Amurka Barry "Butch" Wilmore da Sunita "Suni" Williams za su kwashe kwanaki takwas ne kacal a Tsahar Ƙasa da Ƙasa da ke Sararin Samaniya ISS. Amma, wata matsala da aka samu a jirgin sama-jannati ta sa sai da suka shafe kwana 288 suna rayuwa a sararin samaniya.

Sun yi ta shawagi a inda babu nauyin maganaɗisun duniya, ta yadda a hankali jikinsu ya dinga sassauyawa daga tsarinsa na dokokin rayuwa. A lokacin da suka sauka a gaɓar tekun Florida, ba a kan dandaryar ƙasa kawai suka sauka ba, sun dawo ne cikin yanayin rayuwar da suka fi sabawa da ita wacce kuma aka tsara su a kanta.

Matsalolin da zama a Sararin Samaniya kan jawo

A yanzu, daɗewa a sararin samaniya ba burika ba ne masu tsawo wajen ganin an cim musu. Mataki ne na ci gaba a binciken sararin samaniya. Sai dai ƙalubalensa na da yawa. Jikin ɗan’adam, wanda aka tsara shi ya rayu a kan ƙarfin maganaɗisu, yana bujire wa rashin ƙarfin maganaɗisun da ke sararin samaniya.

Duk kuwa da motsa jikin da suke yi na awanni biyu na motsa jiki kowace rana — da ƙoƙarin samar da ƙarfin maganaɗisu da gudu a kan injin motsa jiki na treadmill — gangar jikin ba ta samun ƙarfin da ya kamata. Tsokar jiki kan sake. Ƙarfin ƙasusuwa na raguwa saboda rashin sinadarin calcium, inda suke yin rauni sosai kuma da gaggawa ta yadda tsufan da ya kamata a cewa sai a gomman shekaru zai bayyana, yake nunawa a jikin mutum a cikin watanni kaɗan.

Masana sun ce tsoka da ƙasusuwan jikin ɗan’adam da ke taimakawa wajen ba shi ƙarfi da iya tsayawa waje ɗaya na iya daƙushewa sosai a sararin samaniya, saboda ba a motsa su yadda ya dace a can saboda rashin ƙarfin maganaɗisu.

Mujallar Canadian Medical Association ta ce nauyin tsokar jiki na iya raguwa da kusan kashi 20 cikin makonni biyu da kuma kashi 30 cikin watanni uku zuwa shida.

Dr. Ariel Ekblaw, wanda ya kafa shirin MIT Space Exploration Initiative, ya ce jikin Wilmore da Williams zai sake komawa tsarin nauyin maganadinsu na duniya.

"Lokacin da kake rayuwa tsawon lokaci a wajen da babu ƙarfin maganaɗisu, to kana rasa nauyin tsokar jikinka ne. Zuciyarka tana yin rauni saboda ba ta harba jininka sakamakon rashin ƙarfin maganadisu. Hatta yanayin ganinka ka iya sauyawa saboda tsarin ƙwayar idonka tana sauyawa kaɗan a wajen da babu ƙarfin maganadisu,” in ji Ekblaw.

Jikin da ya manta

Watangaririya ita ce hanyar motsawa ba ƙaƙƙautawa saboda rashin ƙarfin maganadisu. Babu nauyi kwata-kwata, ji za ka yi komai shafal da sauƙi. Amma wannan sauƙin na wahala ne. Ba tare da yana iya riƙe kansa ba, jiki sai ya manta da yadda tsarinsa yake.

A doron duniyar Earth, ko tsayuwa mutum ya yi sai tsoka ta mommotsa. A sararin samaniya, tsoka kan zama kusan mara amfani. Bincike ya nuna cewa ƙasusuwa suna shan wahala sosai. Kowane wata da za a yi a yankin da babu ƙarfin maganadisu to ƙarfin ƙashi na raguwa da kashi ɗaya cikin ɗari.

A cikin shekara guda za a yi asarar da za ta kai ta shekaru goma. Sinadarin calcium yana shiga cikin jini, yana ƙara haɗarin kamuwa da cutar ƙoda.

Sannan sai maganar kai. Ruwa yana hawa sama, yana kumbura ƙwaƙwalwa, yana matsar idanu. Wasu ‘yan-sama-jannati idan suka dawo ganinsu yakan yi rauni, ba sa iya gani da mai da hankali kan abu sosai kamar yadda suka saba.

"Yana da matuƙar wahala lokacin da kake a sararin samaniya kuma ka dawo duniya da yadda nauyin jikinsa yaka a da ba tare da raguwa ba. Don haka sai ka sa aiki a kan komwa daidai. Ƙarfi abu ne mai kyau, amma zai ɗauki watanni kafin ka dawo da cikakken ƙarfi," in ji tsohon ɗan-sama-jannatin NASA Jack Fischer a hirarsa da NPR.

Lokaci mai tsawo kafin a saba

Karfin maganadisun duniya ba ya maraba da su in sun dawo gida — yana matsa musu su ji wani bambaraƙwai. Kwanakin farko su kan kasance ganinsu yana dusu-dusu, da rashin daidaito a jiki da tashin zuciya, sai kuma jiki ba ya bin umarnin da ya dace da tsarin halittarsa.

Yin tafiya kan zame musu baƙon abu. Hannaye suna nauyi da rashin karsashi. Warkewa daga wadannan abubuwan kan dauki lokaci mai tsawo kuma mai wahala da rashin tabbas.

Ɗaya daga cikin abubuwan ban mamaki na rashin nauyi shi ne ‘yan-sama-jannatin sukan ƙara tsawo yayin zamansu a sararin samaniya, wani lokaci har zuwa inci biyu. Tun da nauyin maganadisun duniya ba ya matsa wa ƙashin baya, ƙashin da ke tsakanin ƙasusuwan bayansu na faɗaɗa, suna tsawaita ƙasusuwan bayan.

Duk da cewa wannan canjin na ɗan lokaci ne kuma suna dawo da tsayinsu na gaske lokacin da suka dawo duniya, NASA ta ce ƙwayoyin halittar dabi’u da na wajen zama wato epigenetics suna taka rawa a cikin sauye-sauyen da mutane ke fuskanta a sararin samaniya.

Canje-canje a cikin bayyana kwayoyin halitta da sauye-sauyen tsarin garkuwar jiki suna kasancewa alamun tafiyar sararin samaniya da ba sa gushewa gaba ɗaya.

Hanyar Zuwa Duniyar Mars

NASA da sauran hukumomin sararin samaniya tuni sun fara rige-rigen zuwa Mars, tafiyar da za ta ɗauki shekaru, ba watanni ba. Bayanai daga waɗannan dogon lokaci suna da matuƙar muhimmanci, amma tambayar ita ce: Shin jikin mutum zai iya jurewa?

Shin zai iya tsira daga yiwuwar lalacewa sakamakon kutsawa can cikin sararin samaniya ta yadda ba zai dawo daidai ba?

Kowane ɗan-sama-jannati da ya dawo yana bayar da wata alama. Kowane mataki da suke ɗauka, mai rauni amma mai ƙuduri, wani darasi ne a cikin iyakokin juriya na ɗan’adam. Dawowarsu ba yana nufin aikin ya ƙare ba ke nan.

Likitocin NASA za su ci gaba da duba Wilmore da Williams don gano ko suna da alamun cutar kansa har tsawon rayuwarsu.

A gare su, a yanzu ne gwajin na gaske da gwagwarmayar dawo da kansu yadda suke a baya ya fara.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us