Daga Sylvia Chebet
Da zarar an kaɗa ƙararrawa, karnukan za su fara dalalar da yawu a wani gwaji da aka yi na Pavlovia, wanda ya ƙunshi amfani da salon zaburarwa a tsarin saita halayya.
Bikin Dogtober, bikin shekara-shekara da ke haɗa kan masu kare da karnukansu na rana guda ta farin ciki da abota, tamkar "zobe” da ke sanya annashuwa a zukatan karnuka a Nairobi.
"Na taso tare da karnuka. Ina ƙaunar su matuƙa," cewar wata mazauniyar Nairobi Sylvia Mati a zantawa da TRT Afrika.
"Suna buƙatar ƙauna da kula, kamar dai mutane. Kamar yadda masu magana kan ce, 'Jelar kare ba ta ƙarya'. Idan ka shigo gida, jelarsa ba ta daina kaɗawa, hakan na nufin karenka na murnanr ganin ka."
A wajen Mati, babu abin da ya fi ban takaici ka ga ana zaluntar karenka. "Yana ƙona min rai," in ji ta.
"Ba na tunanin a ce mutum ya ɗauki dutse ya jefi kare. Akwai mau kare da ke rufe su tsawon rana, saboda wai karnukan gadi ne."
Mati tana amfani da bikin Dogtober a matsayin damar wayar da kai kan tausayawa kare da muhimmancinsu a rayuwarmu.
Kula da kere
A matsayinta na ƙwararriyar mai shiray biki, shirya bikin Dogtober na Nairobi abu ne mai sauƙi ga Mati.
Mati ta ce, "Ana yin bikin Dogtober duk shekara a Australia, AMurka da wasu ƙasashe da yawa. Shi ya sa na ce mai zai hana mu kawo bikin Dogtober zuwa Kenya?".
Wannan shekara 10 baya kenan. Mati tana al'ajabin nasarotin da ta samu, "Wannan shekarar shi ne karo na 10."
Baya ga ƙaunar kare
Burin Mati kan karnuka ya maishe ta ƙwararriya kan kare da lafiyarsu da walwalarsu, wanda abu ne da yawancin masu kare ke mantawa.
"Ko ka san cewa albasa tana cutar da kare?" ta tambaya. "Don haka, idan abincinka soyayye ne kuma ka ba wa kare, za ka ɓata cikinsu. Cakulet ma haka."
Mati ta gano cewa yawancin karnuka ba sa son madara, wanda abu ne da wasu masu kare ba su da masaniya kai.
"Za ka ga mutum ya samo ɗan kwikwiyo sai kawi ya nemi madara ya ba shi. Ba haka ake yi ba," ta yi gargaɗi. To wane abinci ban da nama za ka ba kare?
"Karnuka suna son karas, broccoli, kabeji," in ji Mati. Ana gayyato masu sayar da abincin dabbobi zuwa bikin Dogtober Fest don baje kolin hajarsu.
Mati ta yi nuna kan cewa kula da yawan abinci da ake ba wa kare yana da muhimmanci. Kuma ka da a manta da motsa jikinsu.
Damarmakin talla
Bikin Dogtober na Nairobi ya zamo wajen masu samar da ayyuka a fagen kiwon dabbobin ado suke zuwa don neman kwastomomi. baya ga kamfanonin abincin dabbobi, da masu ba da kula, da masu taya kiwo.
Ƙungiyar Kenya Society for the Protection & Care of Animals, daga can ne Mati ta ɗauko karenta na farko a 2010, kuma tana halartan tarukansu.
"Su ne masu ceto karnukan da aka yasar a tituna. A yanzu suna da karnuka sama da 300 na ɗauka," in ji Mati.
Bisa tsari, karnuka suna buƙatar keji da filin da aka ware musu.
"Muna da wurare kaɗan a Nairobi. likitocin dabbobi suna bayar da wajen ajiya. Idan ka yi tafiya, za a kula da karenka da ba shi abinci da fita da shi yawo," in ji Mati. Da tana aikin fita da kae, inda take samun har dala $10 duka awa.
Mati ta faɗa wa TRT Afrika cewa, "Harka ce mai ruɗani saboda masu kare da ke kula da su suna tsoron yarjewa mutane”.
A yanzu Mati tana da kare jinsin Jack Russel Terrier da kuma Kenyan Shepherds guda uku. "Kenyan Shepherds su ne karnukan gida: karnuka ne masu matuƙar biyayya da ba da kariya ," in ji ta.