A wannan ranar sada zumunci ta duniya, wadda ake bikinta a duk faɗin duniya a ranar 30 ga Yulin shekara, mutane suna aika saƙonni masu ratsa zuciya, suna yi tabo abokai don jin ya suke, da kuma musayar hotuna masu tuna baya.
Rana ce daaka amince da ita a hukumance a yayin Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 2011, wanda ya samo asali tun 1958, lokacin Masu gagwarmayar Abota a duniya suka ba da shawarar kebe ranar don murnar abokantaka.
Wannan rana tana ƙarfafa wa mutane a duk faɗin duniya don su ƙaunaci abokansu, nuna godiya, da ƙarfafa dangantakar da ta haɗa mu waje guda.
Amma a duniyar yau da ke da hanyoyin sadarwa da yawa na yanar gizo ya sanya ake yin wasu tambayoyi: Shin da gaske muna da alaka ko kadaici fiye da kowane lokaci?
Duk da ɗimbin shafuka da dandalin sada zumunta na intanet, manhajojin aika saƙonni, da kuma kiran bidiyo waɗanda suka canza yadda muke mu'amala, masana sun yi gargaɗin cewa muna iya yin kuskuren daukar sadarwa da haduwa tare.
"Mutane halittu ne na zamantakewa. Suna buƙatar mu'amala ta fuska da fuska, su kalli idanun juna, su taɓa juna, su kasance a zahiri," Fazilet Seyitoglu, masaniyar ilimin halayyar ɗan adam, ta shaida wa TRT World.
Seyitoglu ta kwashe sama da shekaru goma yana binciken tasirin amfani da yanar gizo don sadarwa ga kwakwalwa , kuma ya rubuta litattafai kan jin dadin ruhi.
Tunani na haɗin kai na dijital kuma ya rubuta littattafai kan jin daɗin rai. Ta yi tsokaci kan salon zamantakewa da da dama da tasirinsu a kan mutane.
"Mutane na bayyana a sigar zamantakewa; suna mu’amala a Facebook, Twitter, Instagram. Amma waɗannan ba nau'ikan hulɗar da ke gamsar da rai ba ne," in ji ta.
"Lokacin da zuciyarku ta yi zafi ko kuna buƙatar wani ya zauna kusa da ku amma ya yi shiru, babu wata manhaja da za ta iya yin irin wannan zumunci."
Cin karo da juna tsakanin shekaru masu alaƙa
Tare da kusan mutane biliyan 5 a kan ynar gizo, kuma sama da biliyan 2.5 suna amfani da kafofin watsa labarun yau da kullum, ɗan adam na mu’amala da juna ta hanyar sadarwar yanar gizo fiye da kowane lokaci.
Amma nazari da bincike na nuna tashin hankali game da rahotannin kadaici, musamman a tsakanin matasa.
A wani bincike da aka gudanar a 2022 wanda masanin ilimin halayyar dan adam Eric J Moody ya jagoranta, daliban jami'a wadanda suka saba yin tattaunawa ta fuska da fuska ba sa fuskantar matsalar kadaicin zuci da na zamantakewa.
Sabanin haka, masu amfani da intanet sosai kuma sun sami ƙarancin kaɗaici na zamantakewa amma suna da kaɗaicin zuciya mai yawa - kadaicin da babu wani adadi na amfani da allon kwamfuta da zai kawar da shi,
Seyitoglu ta yi nuni da wannan sabani da cewa:
"Duniyar yanar gizo na tafiya da sauri. Mutane na neman jin daɗi, amincewa, da kuma gamsuwa nan take. Fage ne da son zuciya ke haddasa shi, ba wai tausayi ba.
Wannan shi ne dalilin da ya sa muke ganin rushewar abokantaka ta gaske, tsakanin bangarori biyu, "in ji ta.
Seyitoglu, ta kara da cewa matsalar ta wuce batun allon amfani da yanar gizo. "Muna rasa wani abu mai daraja, dabi'un al'ummomin Gabas da suka nun muhimmanci ga al'umma, iyali, da kuma dangantaka mai tsawo.
A yau, kowa bukatarsa ya sanya a gaba. Jin dadinsa nan da nan. Rayuwa shi kadai. Kuma ran mutum na fama da wata yunwa, "in ji ta.
Ta bayar da cikakken misali don bayyana al'amura guda biyu waɗanda ke nuna abokan yanar gizo ba za su yi nasara kan na zahiri ba, musamman a lokacin rikice-rikice. Dalilan na iya bambanta duba ga halayyar mutane.
"A lokutan rikici, abokinka na Facebook ba zai iya zuwa kofar gidanka ba. Suna zaune a wani bangare na duniya.
“Komai yawan masoyanka a yanar gizo, ba za ka taba kwatanta su da wadanda za su rike hannayenka ba a lokacin da kake kuka."
Damuwarta ba ta falsafa ba ce kawai. Nazarin Engelberg da Sjöberg na (2004) sun danganta yawan amfani da yanar gizo da karancin daidaita zamantakewa da hankali.
Wani bincike na 2014 da Yao da Zhong suka yi ya gano cewa jarabar amfani da yanar gizo na iya haifar da kaɗaici, ba magannin sa ba.
Kira don sake gano juna
Don haka menene muke yi a cikin duniyar da ke cike da hayaniyar yanar gizo da hulɗa a matakin samaniya?
Seyitoglu ta ce: "Abota ta gaskiya na iya fara wa ta hanyar yanar gizo, amma dole ne ta habaka a duniya ta zahiri.
“Abota ta gaske na nufin sadaukarwa, lokaci, da kuma kasancewa a zahiri. Idan ba tare da wadannan ba, muna fuskantar hatsarin zama baki har ma ga kawunanmu."
A cikin al'ummar da har ma da tsofaffi ke komawa ga intanet don ƙulla abokantaka da samun abokan hira, Seyitoglu ta yi kira ga koma wa ga ciyayye, tattaunawa ta gaske, ziyarar ba zata.
Yayin da yawan kadaici a duniya ke ƙaruwa, yanzu wasu gwamnatoci sun amince da shi a matsayin matsalar kiwon lafiyar jama'a, kalaman na Seyitoglu sun yi tasiri sosai.
Ta kara da cewa "Tabawa shi ne mutum. kallon juna da idanu na warkarwa. Dole ne mu tuna cewa ganin mutum ba daidai yake da sanin sa kawai na.”
A cikin duniyar da ke cike da labaran da aka tace - watakila mafi girman abin da za mu iya yi shi ne mu fito karara - ba tare da kari ko ragi ba ga juna ba.
Saboda haka, a yayin da kuke danna allon wayarku ko na’ura mai kwakwalwa don duba me ya faru a baya d ama kawancen yau, ku duba yiwuwar ajiye allon tare da kiran wani - ko ma ku hadu da su fuska da fuska.
A yayin da duniyar yanar gizo ke hada ku da mutane, gana wa a zahiri ce za ta tabbatar da cewar kun mallaki juna.
A wannan Rana ta Aboka ta Kasa da Kasa, ta bayar da sako na musamman: “A kowacce saniya muna zuba jari a rayuwar yanar gizo, muna kwata daga rayuwarmu ta zamantakewa. Kuma daga baya, za mu fuskanci talauci ba a aljihunanmu ba, sai dai a zukatanmu.”