Ƙungiyar masu sayar da mai da gas a Nijeriya (NOGASA) ta yi gargaɗin cewa idan har Matatar Mai ta Dangote ta ci gaba da shirinta na fara dakon fetur da gas a faɗin Nijeriya da isar da su kai-tsaye ga masu sayarwa maimakon bi ta hannun masu dakon man, to ƙasar za ta fuskanci tarnaƙi wajen samar da mai da ma fama da rashin mai na tsawon lokaci tare da durƙushewar tsarin dakon mai da ƙasar ke bi a halin yanzu.
Shugaban ƙungiyar ta NOGASA, Bennett Koriene ne ya yi wannan bayanin a lokacin taron ƙungiyar na shekara-shekara inda ya ce shirin na Matatar Dangote ba zai haifar da alheri ba.
Tun a watan Yuni ne Matatar ta Dangote ta yi shelar cewa za ta fara dakon mai ga gidajen mai da ma masu amfani da mai da yawa kyauta a faɗin ƙasar.
Kamfanin na Dangote ya ce domin tabbatar da nasarar shirin, ya sayi manyan motocin dakon mai har 4,000.
Kazalika kamfanin ya ce shirin wanda zai fara aiki ranar 15 ga watan Agusta, zai bai wa masu sayen mai da yawa damar iya sayen man a kan bashi.
Wannan matakin na Dangote ya biyo bayan matsalar da matatar ta fuskanta wajen sayar da man fetur da gas ga ‘yan kasuwa a Nijeriya, inda wasu ke shigowa da tataccen mai daga ƙetare maimakon saya daga sabuwar matatar da aka kashe dala biliyan 20 wajen gina ta.
Sai dai kuma a halin yanzu Ƙungiyar NOGASA ta masu sayar da mai da gas ta nemi Matatar Dangote ta dakatar da shirin kuma ta koma teburin tattaunawa domin magance matsalar.
Ƙungiyar ta ce ya kamata Matatar Dangote ta koyi darasi daga matatun man da suka daina aiki a ƙarƙashin gudanarwar kamfanin Mai na Nijeriya, NNPC.
Kazalika, masu sayar da man sun nemi Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu ya sa baki a lamarin, suna cewa dakon mai a faɗin Nijeriya a ƙarƙashin Matatar Dangote ba zai ɗore ba.
A hannu guda kuma, Jaridar Punch ta Nijeriyar ta ambato Shugaban Ƙungiyar Masu Sayar da Man Fetur ga Jama’a a Nijeriya (PETROAN) Billy Gillis-Harry yana cewa ka da ‘yan Nijeriya su yi murna tukunna game da shelar da Matatar Dangote ta yi domin shi ma yana goyon bayan matatar ta dakatar da shirin nata na dakon mai kai-tsaye ga masu sayarwa.
Shi ma Johnson Oboh Peter, Shugaban Kamfanin Mai na Mesh Oil ya yi kira ga Dangote da ya tattauna da duk masu sayar da mai, ya kuma yi watsi da shirinsa na dakon mai a faɗin ƙasar.
Ya ce idan har Dangote ya cim ma yarjejeniya da masu sayar da mai, babu wanda zai dinga shigo da tataccen mai daga ƙetare.
Sai dai kuma masana sun ce samun irin wannan gogayyar a kasuwa na iya zama alheri domin za ta sa kowa ya yi ta ƙoƙarin sauƙaƙa farashinsa ta yadda mutane za su fi son sayen mai daga waje mai sauƙi.