Shin ya kamata Nijeriya ta dinga yin duka zaɓukanta a rana ɗaya?
SIYASA
3 minti karatu
Shin ya kamata Nijeriya ta dinga yin duka zaɓukanta a rana ɗaya?Wannan daya ne cikin sauye-sauyen da ake kokarin kawowa yayin da majalisun dokokin Nijeriya suke aikin gyara ga tsarin mulkin kasar na 1999.
Shin ya kamata Nijeriya ta dinga yin duka zaɓukanta a rana ɗaya? / Reuters
30 Yuli 2025

Ko akwai hikima idan Nijeriya ta koma tsarin gudanar da manyan zabuka a lokaci guda kuma a rana guda? A nan ana nufin cewa a yi zaben shugaban kasa, da na gwamnoni, da na sanatoci, da na majalisun tarayya, da na majalisun jihohi duka a rana daya.

Wannan daya ne cikin sauye-sauyen da ake kokarin kawowa yayin da majalisun dokokin Nijeriya suke aikin gyara ga tsarin mulkin kasar na 1999.

Ga yadda abin yake:

A manyan zabuka da ake gudanarwa duk bayan shekaru 4 don kawo sabbin jagororin mulkin siyasa a fadin Nijeriya, akan gudanar da zabukan na matakan tarayya da na jihohi a lokuta daban-daban, inda akan ba da tazarar mako daya ko biyu tsakanin zabukan.

A shekarun baya-bayan ana gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisun tarayya ne da farko, sannan daga bisani a yi zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi. Amma fa a shekarar 1999, zabukan jihohi aka fara yi kafin aka yi na matakin tarayya.

Dalilin yunkurin fara yin zabuka a rana guda shi ne a rage tsadar gudanar da zabuka a Nijeriya, a bangaren gwamnati, da ‘yan siyasa, da jam’iyyu, da ma cibiyoyin da ke taimakawa wajen aiwatar da zabukan.

Da yake gabatar da ƙudurin, Sanata Mustapha daga jihar Kwara wanda dan jami’yyar APC mai mulkin kasar ne, ya nuna rashin jin daɗinsa game da yadda kuɗin da ake kashewa wajen gudanar da zaɓe ya ƙaru daga naira biliyan 1.5 a shekarar 1999, zuwa naira biliyan 350 a shekarar 2023.

Sanatan ya ce idan aka yi la’akari da ƙasashe irin su Amurka da Indiya da Brazil, inda ake gudanar da zaɓuka a rana ɗaya, za a ga irin alfanun da hakan zai kawo wa kasa kamar Nijeriya.

Shi ma Sakataren yada Labarai na kasa na jam’iyyar NNPP, Ladipo Johnson, ya ce yin zabuka rana guda zai rage kashe kudi da kar ingancin zabukan.

Ya ce “idan aka yi zabuka rana guda, duka ‘yan takara za su hada karfinsu tare a rumfunan zabe don kula da yadda ake kadawa da fitar da sakamakon zabukan.”

Haka ma Sakataren yada Labarai na kasa na jam’iyyar Labour Party, Obiora Ifoh, ya ce kudurin zai kawar da karkasa zabuka da rage tasirin yin zaben amshin shata, wanda ya ce takan faru bayan an yi zaben Shugaban Ƙasa da farko, idan an zo zaben gwamnoni, masu zabe kan koma zabar jam’iyyar da ta yi nasara a sama.”

Sai dai shi kuwa mataimakin shugaban matasan jam’iyyar PDP, Timothy Osadolor ya yi maraba da kudurin amma ya yi gargadin ka da a yi yaudara.

Kamar dai yadda aka ambato Sakataren yada Labarai na kasa na jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, yana fada.

Sai dai kuma, yayin da wasu ke goyon bayan ƙudirin, wasu na ganin bai kamata a sauya dokar zaɓen ƙasar ba da wannan manufa.

Sanata Adams Oshiomhole mai wakiltar jihar Edo, wanda shi ma dan jami’yyar APC mai mulki ne, ya ce duk da cewa kudirin na da manufa mai kyau, gudanar da zaɓuka rana ɗaya zai iya haddasa matsalolin gudanarwa, wanda shi kuma zai iya raunata amincin da sahihancin zaɓukan.

Amma fa ba Oshiomhole ne kawai ya nuna rashin gamsuwa da ƙudirin ba.

Mataimakin sakataren gudanarwa na ƙasa na jam’iyyar APC, Nze Chdi Duru, ya ce gudanar da zaɓukan gabaɗaya a rana ɗaya zai buwayi hukumar zaben kasar.

Ya ƙara da cewa gudanar da zaɓukan cikin ranaku mabambanta shi ke hana durƙushewar tsare-tsaren hukumar zaɓen.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us