Mesut Ozil, wani ɗan wasa ne da ba za a manta da shi a tarihi, musamman a zukatan masoya Real Madrid da Arsenal, da ma wasu ƙungiyoyi a Jamus da Turkiyya.
An haifi Mesut Ozil a birnin Gelsenkirchen na Jamus, kuma iyayensa Turkawa ne mazauna Jamus.
Kakansa Baturke ne da ya je ƙwadago Jamus ta Yamma, wanda ya sa Ozil ke yawan ambaton tushensa na Turkiyya.
A tarihin ƙwallo a Turai, Mesut Ozil shi ne ɗan wasa ɗaya tilo da ya taɓa zama wanda ya fi kowa ba da tallafin cin ƙwallo, wato assists a kaka guda.
Ya kafa wannan tarihin a gasannin Firimiya, da LaLiga, da Bundesliga, da gasar Zakarun Turai ta UEFA, da gasar Europa, da gasar Kofin Duniya, da kuma gasar Kofin Duniya ta Ƙungiyoyi.
Ozil ya yi zarra wajen iya ba da ƙwallo, da aiko fasin, da nuna tsabar basirar fahimtar dabarun mamaya a filin wasa, ta amfani da ƙwaƙwalwa maimakon ƙarfin tuwo kawai.
Muhimmancin ba da tallafin ƙwallo
A ƙwallo ƙafa, tallafin cin ƙwallo na nufin wanda ya yi bugu na ƙarshe kafin wanda ya ci ƙwallo ya zura ƙwallon a raga.
Ana ƙidaya ba da tallafin cin ƙwallo a matsayin abin bajinta ne saboda fasin ɗin ya haifar da nasarar zura ƙwallo.
Sannan hakan na nuna ƙoƙarin ɗan wasan wajen samar da damar ci, da nuna kaifin basira, da rashin son-kai, musamman idan yana da damar gwada sa'arsa amma ya zaɓi bayar da fasin.
Gwanayen ba da tallafin cin ƙwallo su ne sirrin nasarar ƙungiyoyi da dama, saboda su ne ruhin haɗin-kan ‘yan wasan gaba.
Duka wannan sun sa ana ƙirga tallafin cin ƙwallo don gano darajar ɗan wasa a tawaga, da kuma a kasuwa cinikin ‘yan wasa.
Zarra a ƙasashe daban-daban
Mesut Ozil ya fara shuhura ne a gasar Bundesliga ta ƙasarsa Jamus, a ƙungiyar Werder Bremen bayan ya baro Schalke 04 a Janairun 2008.
Ya tafi Real Madrid a 2010 kuma ya lailaya ƙwallo tare da taurari irinsu Cristiano Ronaldo, inda ya buga wasa a matsayin ɗan wasan tsakiya mai kai farmaki, inda ya taimaki Madrid wajen lashe tarin kofuna.
A Satumban 2013, Arsenal ta sayo Ozil kan euro miliyan 50, inda ya zama ɗan wasa mafi tsada da ƙungiyar ta taɓa saya a tarihinta na wancan zamanin.
Ozil ya nuna bajinta a farkon zamansa a Arsenal, inda ya taimaka wajen kawo ƙarshen kamfar lashe kofi a ƙungiyar, har suka ɗaga kofin FA Cup a 2014, da 2015, da ma 2017.
Sai dai zuwa ƙarshen zamansa a Arsenal, tagomashin Ozil ya fara yin ƙasa inda ya dingi shan suka daga mahukunta da wasu masoya ƙungiyar.
Daga nan dangantaka ta yi tsami tsakanin Ozil da Arsenal, saboda dalilai da dama, ciki har da yadda Ozil ya nuna goyon baya a fili ga gwagwarmayar Falasɗinawa da mutanen Uighur, batun da rahotannin suka nuna bai yi wa kocin Arsenal Mikel Arteta daɗi ba.
Sauran ƙungiyoyi
A 2021, Mesut Ozil ya bar Arsenal ya koma ƙasar da ke kusanci da zuciyarsa, wato Turkiyya, inda ya buga wa ƙungiyoyin Fenerbahçe da kuma İstanbul Başakşehir.
Sai dai jinya da kuma gajiyarwar shekaru sun cim masa, har zuwa lokacin da ya yi ritaya daga ƙwallo a 22 Maris ɗin 2023.
Mesut Ozil ya kasancewa muhimmin ɗan wasa a tawagar Jamus wadda ta lashe Kofin Duniya na FIFA a 2014 da aka buga a Brazil, inda ya buga duka wasanni 7 na tawagar ta buga.
Ya yi murabus daga bugawa tawagar ƙasarsa Jamus a Yulin 2018, bayan da ƙasar da gaza wuce matakin rukuni a gasar Kofin Duniya ta 2018 da aka yi a Rasha.
Siyasar Turkiyya
Da ma can an daɗe ana alaƙanta Ozil da Turkiyya da kuma Turkawa, ba wai kawai saboda shi asalin Baturke ba ne, har ma saboda kusancinsa da fitattun mutane a Turkiyya.
Ko a 2018, Ozil ya wallafa hotonsa da shugaban Turkiyya, wanda ya haifar da cecekuce a Jamus. Haka nan a 2019, Shugaba Erdogan ya halarci ɗaurin auren Ozil da aka yi a birnin Istanbul.
A farkon 2025, Mesut Ozil ya shiga siyasa gadan-gadan, inda ya shiga jam’iyyar shugaba Erdogan mai mulki ta AK Party.
Ya samu muƙami cikin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ta AK Party, wato MKYK a watan Fabrairun 2025.